Shugabannin kasashen Afrika su na ci gaba da kokawa da karancin alluran rigakafin coronavirus daga kasashe masu arziki. Shugaba na baya-bayan nan da ya yi magana akan wannan matsala shi ne Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukradiyar Congo. A hira da wakilin VOA Marius Mugunga, shugaban ya kuma yi tsokaci game da yaki da ta’addanci a nahiyar Afirka.
Shugabannin Kasashen Nahiyar Afirka Na Kokawa Da Karancin Allurar Riga-kafin COVID-19
Your browser doesn’t support HTML5
Matsalar tsaro da annobar COVID-19, na daga cikin manyan kalubalen da suke haifar tarnaki ga kasashen nahiyar Afirka da dama, kamar yadda shugaban Jamhuriyar Dimokradiyar Congo Felix Tshisekedi ya ce.