A birnin Jos da ke jihar Filaton Najeriya, kabilu da mabiya addinai daban-daban ne ke zaune a tare tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka. Amma shekaru 20 kenan birnin yake ta fama da rikice-rikicen masu nasaba da addini da kabilanci kamar yadda ya auku cikin watan Agustan da ya gabata. Yanzu haka wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun yi hobbasan kawo karshen irin wadannan rigingimu. Ga Iliyasu Kasimu da karin bayani.