Shugaban kasar Nijar wanda kuma shi ne shugaban kungiyar kasashen biyar shi ya bude taron da jawabi na musamma.
Wannan kungiyar dai an kafata ne a shekarar 1959 da nufin bunkasa tattalin arziki da bada damar zirga ziega ga al'ummomin kasashen.
Saidai yadda matsalar Boko Haram a Najeriya da rikicin azbinawan Mali suka ta'azara sun sa shugabannin kungiyar bada fifiko akan batun samar da tsaro.
A cewar ministan tsaron kasar Nijar Kanar Ibrahim Yakuba yace shugaban kasa yace sai an nemi dabaru da suke daidai da irin ta'adancin yanzu kafin a cimma nasara. Dalili ke nan ya bada shawarar kafa dakaru na musamman da zasu samu horon da ya yi daidai da halin da ake ciki yanzu.
Sun kafa irinta a kan iyaka da Najeriya da Chadi. Suna kuma neman izini su kafa wata a iyaka da Mali kodayake akwai sojojin kasashen duniya kusan dubu 15 amma Nijar bata samu saukin hare-haren 'yan Mali ba..
Kwararrun kasashen sun gabatar da muhimman shawarwari ga shugabannin wannan kungiya domin dorewar ayyukan da aka sa gaba.
Issoufou Isa, mataimakin sakataren zartaswa na kungiyar yace sun basu shawara akan abun da suke son yi, kamar gina manyan otel kowasu wuraren aiki da zasu kawowa kungiyar kudi.Zasu gina rijiyoyi domin bada ruwan sha da hanyoyi da kuma yin anfani da zafin rana domin samun wutar lantarki.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5