Shugabannin Kananan Hukumomi 17 Sun Kalubalanci Matakin Gwamnan Filato Na Dakatar Da Su

Shugabannin Kananan Hukumomi 17 Sun Kalubalanci Matakin Gwamnan Filato

Shugabannin kananan hukumomi goma sha bakwai da daukacin kansilolin jihar Filato sun kalubalanci matakin da gwamnatin jihar ta bi, na dakatar da su daga mukamansu.

A makon jiya ne gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya amince da shawarar da Majalisar Dokokin jihar ta aike masa, na ya dakatar da shugabannin kananan hukumomin jihar, don gudanar da bincike kan shiga da fitar kudaden kananan hukumomin.

A taron manema labarai, shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin a jihar Filato, Miskom Alex Na'antwan, wanda shine shugaban karamar hukumar Shendam, ya ce sun sami takardar gayyata daga Majalisar Dokoki, amma kafin su tattara bayanansu sai suka ga takardar dakatar da su a kafafen sada zumunta na zamani, bisa amincewar gwamnan jihar.

Suma kansilolin jihar sun gudanar da taron manema labarai, inda suka ce, gwamna bashi da ikon dakatar da su daga mukaminsu domin suma zababbun wakilai ne.

Hon John Dashe, shine shugaban kungiyar kansiloli a jihar filato ya ce suna bukatar gwamna a matsayinsa na masanin doka, ya janye matakin da ya dauka.

Lauya mai zaman kansa a Jos, barista Yakubu Sale Bawa, ya ce doka bata ba gwamna ko majalisa hurumin dakatar da shugannin kananan hukumomi ba.

Kotu ce kadai za ta warware wannan takaddama, yayin da tuni wata majiya ta ce gwamnati ta zayyana sunayen wadanda za ta baiwa shugabancin riko a kananan hukumomin.

Domin Karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabannin Kananan Hukumomi 17 Sun Kalubalanci Matakin Gwamnan Filato Na Dakatar Da Su - 3'52"