Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da suke kokarin kara damammakin samun yarjejeniyar da za su yi amfani da ita wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi a taron Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi dake gudana a kasar Azerbaijan
Tunda fari, kasar dake karbar bakuncin taron sauyin yanayin mai taken “COP29” ta roki kasashen na G-20 dasu aike da kyakkyawan sako akan bukatar shawo kan matsalar sauyin yanayi tare da samar da ikon da zai taimaka wajen ceto batutuwan da aka tattauna a birnin Baku, na Azerbaijan daga dulmuyewa cikin tabo.
A yayin da duniya ke dosar shekara mafi zafi a tarihi, shugabanni na kokarin su tallafa wajen samar da martanin kasa da kasa akan sauyin yanayi tun gabanin Donald Trump ya sake karbar ragamar shugabancin Amurka a watan Janairu mai zuwa. rahotannin sun ce yana shirye-shiryen rushe manufar Amurka akan dumamar yanayi tare da ficewa daga gagarumar yarjejeniyar nan ta birnin Paris.
A jiya Litinin, taron Shugabannin G-20 da yanzu haka ke gudana a birnin Rio De Janairo, na kasar Brazil, ya bukaci a samar da sanarwar hadin gwiwa domin “gaggauta kara samarda makudan kudaden yaki da sauyin yanayi daga bilyoyi zuwa tiriliyoyin daloli daga dukkanin hanyoyi” da nufin yin martani ga dumamar yanayi.
Haka kuma sun bukaci masu shiga tsakani a taron COP29 su cimma matsaya akan sabuwar manufar kudade dangane da yawan kudaden da mawadatan kasashe zasu baiwa kasashen masu tasowa domin yakar sauyin yanayi, wannan shine babban jigo a tattaunawar da ake yi akan sauyin yanayin.
“Shugabannin G-20 sun aike da bayayyanannan sako ga masu shiga tsakani a taron cop29 cewar: kada ku bar birnin Baku ba tare da cimma sabuwar manufa akan samarda kudade ba. hakan wani al’amari ne “daya shafi kowace kasa,” kamar yadda shugaban yaki da sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya Simon Stiell ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Manufar masu shiga tsakani a tattaunawar sauyin yanayin ita ce samar da cikakken daftari akan yarjejeniyar manufar samarda kudade kan nan zuwa yammacin gobe Laraba, a cewar babban mai shiga tsakani a taron yalchin rafiyev na kasar Azerbaijan.
“Mun kara hanzari a tafiyar,” a cewar Rafiyev.” sakamakon zai zamo kyakkyawa kamar jajircewar bangarorin dake cikin yarjejeniyar da za ta taimaka mana wajen samun mafita.”
-Reuters