Shugaban Amurka Donald Trump da takwaran aikinsa Vladimir Putin sun amince su marawa Majalisar Dinkin Duniya, ko MDD baya, domin a kawo karshen yakin basasan Syria cikin lumana, wanda aka kwashe kusan shekaru bakwai ana yi.
Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce shugabannin biyu sun kwashe sama da sa’a guda suna tattaunawa, inda suka jaddada muhimmancin kawo karshen halin kakani-kayin da kasar ta shiga, inda miliyoyin ‘yan Syria suka rasa muhallansu.
Shugaba Trump da Putin sun ce akwai bukatar a bar mutanen kasar da suka tsere su koma gidajensu, sannan a tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasar ba tare da wata muguwar manufa ba, da kuma kawar da duk wata maboyar ‘yan ta’adda.
Shugaba Trump ya gana da takwaran aikin nasa ne ta waya talho, kwana guda bayan da shugaban Rashan ya tattauna da shugaban Syria Bashar al- Assad, kan yadda za a shawo kan yakin basasan kasar a siyasance, wanda ya lakume rayuka dubu 400.