Shugabannin Afrika Sun Amince Da Amfani Da Hodar DDT

Wadansu yara masu fama da zazzabin cizon sauro suna kwance

Taron kolin shugabannin kasashen nahiyar Afrika da aka yi a birnin tarayyar Abuja kan yaki da tarin fuka da zazzabin cizon sauro da ake kira Abuja+12, ya amince da amfani da hodar DDT
Taron kolin shugabannin kasashen nahiyar Afrika da aka yi a birnin tarayyar Abuja kan yaki da tarin fuka da zazzabin cizon sauro da ake kira Abuja+12, ya amince da amfani da hodar DDT (dichlorodiphenyltrichloroethane), wata hodar kashe kwari da aka haramta amfani da ita a duk fadin duniya shekaru da dama da suka wuce.

Shugabannin kasashen nahiyar Afrikan sun amince da amfani da hodar ne a matsayin hanyar shawo kan zazzabin cizon sauro a nahiyar baki daya.

Ministan lafiya na Najeriya farfesa Onyebuchi Chukwu ya shaidawa taron cewa, hukumar lafiya ta duniya ta bada izinin amfani da hodar a cikin gida kawai domin kashe sauro amma ba a fannin ayyukan noma ba domin gudun illarshi ga muhalli. Ya kuma bayyana cewa, kasashen Namibia da Erithrea suna daga cikin kasashen da suka fara amfani da hodar.

Shugabannin kasashen nahiyar Afrika sun tsayar da shawarar fara amfani da hodar DDT ne saboda sauro baya jin irin magungunan da ake amfani da su a halin yanzu. Shugabannin sun bayyana damuwa cewa, zazzabin cizon sauro, yana kan gaba a cikin cututukan da suke kashe mata masu ciki da kananan yara.

Shugabannin sun kuma tsayar da shawarar daukar matakin rage dogaro ga tallafin da ake samu daga kasashen ketare domin yaki da cutar kanjamau, da tarin fuka da zazzabin cizon sauro.

Shugabannin sun kuma tsaida shawarar rage dogaro ga kasashen waje domin sayen magungunan yaki da cutukan da suke yawan kashe mutane a nahiyar. Misali, kashi 80% na abinda ake bukata a yaki da wadannan cututukan yana zuwa ne daga kasashen ketare, da ya hada da magunguna. Saboda haka suka tsayar da shawarar himmatuwa wajen daukar nauyin yaki da cututukan a maimakon dogara ga kasashen waje.

Shugabannin sun kuma tsaida shawarar bada karfi wajen samar da abinci mai gina jiki ga masu fama da wadannan cututukan saboda maganin zai zama da cutarwa idan babu isasshen abinci. Za a kuma bada karfi kan nazari da bincike.