Shugabannin Afirka Ta Yamma Su Na Taro Kan Boko Haram Yau Asabar A Paris

Shugaba Francois Hollande na Faransa da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya a zauren taron kasa da kasa na Abuja

Shugabannin Afirka ta Yamma su na taro yau asabar a Paris, domin kyautata hadin kai wajen yakar kungiyar Boko Haram, wadda ta sace dalibai mata su fiye da 200 a watan da ya shige, ta kuma gurgunta harkokin yau da kullum a wannan yankin.

Bacin ran da aka nuna kan sace wadannan dalibai ya tilasta ma shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya amince da taimakon AMurka, Britaniya da kuma Faransa wajen nemo wadannan 'yan mata da aka sace.

A makon jiya ne Faransa, wadda ita ma ta fuskanci hare-haren tsagera 'yan bindiga a baya a saboda tsoma hannun sojojinta wajen murkushe masu tawayen addini a Mali, ta sanar da cewa ta shirya taron koli a tsakanin Najeriya da makwabtanta, Chadi, Kamaru, Nijar da kuma Jamhuriyar Benin, dukkansu masu amfani da harshen Faransanci.

Ma'aikatan diflomasiyya na Faransa sun ce sojojin kasashen yammaci ba zasu tsoma hannun sojojinsu ba, amma kuma su na sa ran cewa za a tsara dabara mai nagarta ta murkushe Boko Haram, wadda ta kashe mutane fiye da dubu 5 a kyamfe din da ta ce tana yi da nufin kafa mulkin Islama a yankin.


Wata majiyar diflomasiyya ta Faransa ta ce akwai rashin tattaunawa yadda ya kamata a tsakanin Najeriya da Kamaru. "Kafin wannan lokaci, Kamaru ba ta yarda cewa tana da matsala ba, amma kuma Boko Haram ta shiga arewacinta, yayin da a gabas take fama da matsalar kwararar 'yan gudun hijira daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Tilas ne ta tattauna da Najeriya."

Ana sa ran cewa taron na yau asabar zai sa wadannan kasashe, tare da taimakon kasashen yammaci, su hada kai wajen tattarawa da rarraba bayanan leken asiri, da musanyar wasu bayanai, da inganta tsaron iyakoki domin hana 'yan Boko Haram satar shiga da makamai, tare da zirga-zirga a wannan yanki.