Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani da babban jami'in harkokin mulkin kasar Abdullah Abdullah sun gana da kusoshin gwamnatin Amurka a fadar hutu ta shugaban Amurka da ake kira Camp David dake jiihar Maryland jiya Litinin, wurin da bashi da nisa da nan birnin Washington.
Shawarwarin da suka hada da sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, sakataren tsaron Amurka Ashton Carter, da kuma sakataren baitul mali Jack Lew, an gudanar dasu ne da zummar inganta danganatakar aiki tsakanin kasashen biyu, wacce tayi tsami saboda shekaru 14 da Amurka tayi tana yaki a kasar, da kuma kusan zaman doya da manja tsakanin Amurka da tsohon shugaban Afghanistan Hamid karzai.
Alokacin da suka yi shawarwarin shugabannin sunyi kokarin su yi magana kan batun tsaro d a Shugaba Ashraf Ghani ya nuna. Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter yace Amurka zata bukaci karin kudi domin tabbatar karfin sojojin Afganistan ya dore kan dakaru 352,000 har zuwa shekarar kudi ta 2017.
Sakatare Carter yace kwamandojin sojojin taron dangi da kwamandoji Afghanistan sun bada shawarar a tabbatar karfin jami'an tsaron kasar mai karfi haka domin rage su zai maida hanun agogo baya a nasarori da aka samu ta fuskar tsaro.
Daga bisani shugabannin sun yi taro da manema labarai domin tallata abunda suka kira "farfado da dangataka tsakanin kasashen".