Yayinda shugaban Amurka Donald Trump da mukarabbansa irinsu Sean Spicer, kakakin fadar mulki ta White House, ke ta jinjinawa nasarar da suka ce shugaba Trump ya samu a tafiyarsa ta farko zuwa kasashen ketare, su shugabannin kasashen Turan suna bayyana ra’ayin da ya sabawa na jagabannin Amurka din.
Jim kadan bayan dawowarsa gida daga tafiyar, shugaba Trump ya ce ya karfafa dangatakar dake tsakaninsa da shugabannin Turai. To amma shugabannin kasashen Turan, tun ma ba na Jamus da Faransa ba, suna ganin abin daban.
Da yawansu suna ganin yanzu kasashen ba sa da hadin kan da suke da shi kafin Trump ya zo ya halarci taron kolin da suka kamalla, kuma yanzu sun tabattar da cewa idan wani lamari ya barke, zasu tinkari abin ne su kadai, ba tareda Amurka ba – wanda wannan wani abu ne da basu zaci zai faru ba kafin a zabi Trump.
Da yawa daga shugabannin yanzu suna ganin Amurka ba wata kasa ce da zasu iya dogaro a kanta ba.