Shugabanin Kasashen Kungiyar ECOWAS Zasu Kai Ziyara Mali

Yau Alhamis ,23 ga watan Yuli tawagar wasu shugabannin kasashen Afrika ta yamma a karkashin shugaban rikon kungiyar Ecowas Issouhou Mahamadou na jamhuriyar Nijer za ta isa kasar Mali domin tanttaunawa da bangarorin da ke takaddama da juna da nufin nemo bakin zaren warware rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a wannan kasa.

A makon jiya wasu jami’an shiga tsakani a karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan suka gana da bangarorin da ba sa ga maciji da juna.

taron shiga tsakani na kungiyar CEDEAO

Tawagar ta kungiyar CEDEAO wacce ke kunshe da shugaban rikonta Issouhou Mahamadou na Nijer, da Muhammadu Buhari, na Najeriya da Macki Sall na Senegal, da Nana Akufo Addo na Ghana, da kuma Alassan Ouattara na Cote d’ivoire, za ta gana da bangarorin kasar Mali da ke rikici don ganin an kawo karshen kallon hadarin kajin da su ke yi wa juna a cewar shugaban majalisar ministocin harkokin wajen kasashen ECOWAS Kalla Hankourao.

Tun a washegarin barkewar wannan rikici ‘yan hamayya na kawancen M5 ke matsa wa shugaba Ibrahim Boubakar Keaita akan ya sauka daga karagar mulki, to sai dai kungiyar CEDEAO na ganin wannan magana ba ta taso ba.

A nasu bangaren masu rajin kare dimokradiya irinsu shugaban kungiyar Voix des sans Voix Alhaji Nassirou Seidou, ya fadi cewa kungiyar ECOWAS ta makaro.

Barkewar hatsaniya a kasar Mali wani abu ne da ke barazana ga kasashen Sahel, yankin da a yanzu haka ke fama da matsananciyar matsalar tsaro.

Saurari Karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Ziyarar Shugabanin Kasashen Kungiyar ECOWAS Mali