Shugaban WHO Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayanda Isra’ila Ta Kai Hari Kan Filin Jirgin Yemen

Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus

Babban darektan Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce shi da tawagar sa suna babban filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa dake Sana’a babban birnin kasar Yemen lokacin da Isra’ila ta kai hari.

Harin ta sama ya hallaka akalla mutane uku, wasu da dama kuma sun jikkata.

Wata tawagar manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya karkashin jagorancin Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, suna filin jirgin saman a ranar Alhamis, lokacin da aka kai harin, kuma ma'aikatan MDD na cikin wadanda suka jikkata, a cewar kakakin MDD Stephanie Tremblay.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai farmaki ne kan wasu wurare da dama da ke da alaka da kungiyar Houthi a Yemen, ciki har da filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa dake Sana’a, da tashoshi uku a gabar tekun yammacin kasar.

Rundunar Sojojin Isra'ila daga baya ta shaidawa kamfanin dillacin labaran Associated Press cewa, ba su da masaniyar shugaban WHO da tawagar sa suna filin jirgin saman.

Sama da shekara guda kenan da hare-haren Houthi suke kawo cikas ga hanyoyin sufurin jiragen ruwan kasa da kasa, lamarin da ya tilastawa kamfanoni yin tafiya mai tsawo da kashe kudade masu yawa wanda hakan ya haifar da fargabar hauhawar farashin kayayyaki a duniya.