Shugaban Ukraine Volodmyr Zelenskyy ya ce zai saki wasu daga cikin fursunonin da ke da kwarewa don su taimaka a yakin da kasar ke yi da Rasha.
Ukraine har ila yau tana koyawa mutane yadda za su hada ababen fashewa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito
Yayin da dakarun Rasha ke kara kusantar Kyiv, babban birnin Kyiv mai mutum kusan miliyan uku, magajin garin birnin ya nuna shakku ko har za a iya kwashe fararen hula.
Hukumomi suna kuma bai wa duk wani da yake da ra’ayi makami don kare birnin.
Zelenskyy ya ce an kashe yara 16 sannan an jikkata wasu mutum 45 a mamayar da Rasha ta kai wa kasar.
Sai dai shugaban na Ukraine ya ce an kashe dakarun Rasha sama da 4,500 yana mai kira a ga sauran da su ajiye makamansu su fice daga kasar.
“Kada ku biye wa kwamandojinku, kada ku biyewa farfagandar da ake yi, ku tsiratar da ranku.” Zelenskyy ya ce.
Rashar ta tabbatar da mutuwar wasu dakarunta, amma ba ta fadi adadi ba.
Zelenskyy ya kuma yaba da takunkuman da kasashen yammaci suka sakawa Rasha, yana mai cewa matakin ya sa darajar kudin kasar ta fadi warwas.
Ya kuma yi kira ga kungiyar tarayyar turai, da ta hanzarta ba kasar ta Ukraine dama ta zama mamba a kungiyar.