Shugaban Turkiya Zai Fadada Ayyukan Soji A Yankin Dake Karkashin Ikon Kurdawan Syria

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Biyo bayan nasarar da sojojin kasarsa suka samu a Afrin dake cikin kasar Syria yanzu shugaban kasar Turkiya Erdogan zai fadada ayyukan sojojinsa a wasu garuruwan Syria dake karkashin ikon kurdawa

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana niyarsa jiya Litinin, ta fadada ayyukan soji a wuraren dake karkashin ikon kurdawa a Syria, bayan kakkabe su daga tungarsu dake Afrin.

Erdogan yace dakarun kasar Turkiya zasu tunkari birnin Manbij,da kuma Ayn al-Arab da ake kuma kira kobani a Syrian. Da wadansu garuruwa dake kan iyakar Turkiya da Syria a gabashin tekun Euphrates.

Fadada wuraren kai sumamen na iya janyo rikici da Amurka,kawar Turkiyyar a kungiyar tsaron hadin guiwa ta NATO. Yankin kan iyakar na karkashin ikon dakarun Kurdawa da Amurka ke marawa baya, yayinda aka girke dakarun Amurka a Manbij a yunkurin kakkabe kungiyar IS.

Amurka tana kuma fargaban tabarbarcewar halin rayuwa a Afrin, inda rahotannin ke nuni da cewa, farin kaya basu iya samun ruwan sha mai tsabta.

A halin da ake ciki kuma, hukumomin Turkiya sun tsare wadansu mutane hudu da aka samu da sinadarin hada makaman nukiliya a cikin motarsu.

An gano sinadarin da ake kira Colifonium ne lokacin da aka bincike wata mota a unguwar Pursaklar dake Ankara jiya Litinin a wani yaki da ‘yan fasa kwauri.

“Yan sanda sun ce mutanen hudu suna cikin wani gungun masu aikata laifuka dake niyar sayar da sinadarin da ba safai ake samunshi ba, a kasuwar bayan fage kan kudi sama da dala miliyan saba’in.