Yayin da yake halartar taron kungiyar kasashen Afirka a Afirka ta Kudu kotun laifuka ta kasa da kasa ta bukaci a mika Shugaba Al-Bashir ga ita akan zargin da kotun ta yi masa na cin zarafin dan Adam.
Akan haka ne wata kotu a Afirka ta Kudu ta shirya zaman jin karar yau Litinin ta yanke shawarar ko ta cafkeshi ko kuma ta bari ya tafi. Amma ta bada umurnin kada ya bar kasar har sai ta yanke hukunci.
Amma da misalin karfe goma na safiyar yau agogon Afirka ta Kudu shugaba Umar al-Bashir ya fice daga kasar daga filin jirgin sama da shugabannin kasashen waje ke yin anfani dashi.
Har lokacin da shugaban ya bar kasar kotun bata ma gama zamanta ba. To saidai duk shugabannin da suka halarci taron suna da kariya ta diflomasiya saboda haka da wuya a tsare shugaban. Banda haka shugabannin Afirka sun yanke shawarar kada su sake amincewa da kotun wurin kama wani shugaban Afirka saboda zargin cewa kotun shugabannin Afirka ne kadai take kamawa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5