Shugaban Somaliya ya bayyana yawan sojojin Kenya da kungiyar al-Shabab ta kashe

Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud

Shugaban Somaliya yace kimanin sojojin Kenya 180 zuwa 200 dake cikin ayarin sojojin hadin guiwa na kungiyar kasashen Afirka mayakan kungiyar Islama suka kashe a kudu maso yammacin kasar ta Somaliya watan jiya.

Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana alkalumman ne yayin da yake amsa tambayoyi a kafar tashar talibijan ta Somalia daren Laraba yayin da aka tambayaeshi abun da ya sa ya kasance a addu'ar tunawa da sojojin a kasar Kenya.

Shugaban yace "lokacin da aka ce sojoji 180 zuwa 200 da suke kiyaye zaman lafiya a kasarmu aka kashe, ai abun damuwa ne".

Mai magana da yawun dakarun tsaron Kenya David Obonyo ya yi saurin musanta ikirarin shugaban Somaliyan a wata jaridar Kenyan mai suna 'The Star". Yace watakila ikirarin kungiyar al-Shabab ce ta rudar da shugaban saboda yawan wadanda aka ce an kashe sun fi na kamfani guda..

To saida Kenya bata taba bayyana yawan sojopjinta da aka kashe ba a garin El Adde amma ta amince an kashe mata sojoji da dama.

Ita kungiyar Al Shabab tace ta kashe sojojin Kenya fiye da 100