Yau shugaban matasan Afrika ta Kudu na jam’iyar African National Congress –ANC da ruwa siyasa ke neman hadiyewa, zai san makomar shi kan ko kalubalantar dakatar da shi da jam’yar tayi ta zauni ko babu.
Kwamitin ladabtarwa na jam’iyar ANC zai sanar da shawarar da ya yanke yau kan neman ahuwar da Julius Malema ya yi a kan dakatar da shi da jam’iyar tayi na tsawon shekaru biyar sabili da kokarin rarraba kawunan ‘yan jam’iyar da yayi.
A shekarar da ta gabata ne jami’an jam’iyar suka sami Malema da wadansu shugabannin matasa hudu da laifin shuka gaba da tsatsaguwa tsakanin ‘yan jam’iyar.
Sauran shugabannin ma suna kalubalantar hukumcin da cewa, ba a basu damar kare kansu ba kafin jam’iyar ta yanke hukumcin.
Idan jam’iyar bata saurare su ba, yana yiwuwa Malema da sauran abokanshi su kai kara kotu.