Ana sa ran Putin zai yi balaguro zuwa Paris ranar 19 ga watan nan, ziyarar da zata hada bikin bude wata sabuwar Chocin masu ra’ayin rikau
Mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dmitry Peskov ya fada yau Talata cewa a shirye shugaba Putin yake ya gana da shugaba Hollande a duk lokacin da shugaban na Faransa ke da sarari, yayinda shi kuma Mr. Hollande ya fadi cewa har yanzu a shirye ya ke don ganawa muddin shawarwarin zasu kai ga "karfafa zaman lafiya".
Ranar Litinin ministan harkokin wajen Faransa Jean - Marc Ayrault ya ce Rasha na iya fuskantar zargin aikata laifukan yaki saboda hare-haren da take kaiwa a birnini Aleppo dake arewacin Siriyya.
Mr. Jean-Marc ya kuma ce faransa zata tuntubi mahukunta daga kotun duniya don ganin yadda za a kaddamar da bincike.
Duk da dai Rasha ta sha karyata batun kai hari kan farar hula a Siriyya, tana mai cewa ita fa kungiyoyin ‘yan ta’adda ta auna don goyawa shugaba Bashar al-Assad baya