Biyo bayan bayyanashi da hukumar zaben Nijar CENI ta yi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, Muhammadou Issoufou ya fito ya nemi hadin kan 'yan adawa wurin kafa gwamnatin hadin gwiwa saboda zaman lafiyar kasa.
Manufar shugaban shi ne hada kawunan 'yan kasa da zummar shawo kan mataslolin da suka addabi kasar musamman matsalar tsaro sakamakon aika aikar 'yan ta'ada. Kasashen dake makwaftaka da ita irin su Najeriya,Mali da Kamaru suna fama da ta'addanci.
Shugaban jam'iyyar RDN Fasaha Salisu Muhamman Sabi daya daga cikin kakakin shugaban kasa Muhammadou Issoufou yace shugaban na ganin cewa tunda kasar na fama da matsalar tsaro ya kamata ya ba kowa damar kawo tashi gudummawar da zata kaiga zaman lafiya kasa kuma ta cigaba.
Zabukan da aka gudanar sun haddasa tada jijiyoyin wuya musamman na bangaren adawa dalili ke nan da mataimakin sakataren jam'iyyar MNSD Nasara Ibrahim Hamidu ke cewa kiran da shugaban kasa ya yi kaman babu ruwanshi da kukan 'yan adawa. Kiran baya cikin hadin kawunan 'yan kasa. Idan ma yana da kira, na zuwa a tattauna zai yi
Su kuwa kungiyoyin cigaban dimokradiya suna ganin kiran na shugaban tamkar riga malam masallaci ne domin kotun shari'a bata tabbatar da zaben shugaban ba. Kamata ya yi ya jira sai kotun ta yanke shawara. Bayan kotun ta tabbatar masa sai ya kira 'yan adawa ya nemi shawarwarinsu akan yadda za'a bi a gudanar da mulkin kasar.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5