Shugaban Nigeria Muhammad Buhari ya karbi bakuncin shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a fadarsa.
Wannan ziyarar ta shugaban Afirka ta Kudu it ace irinta ta farko da zai kawo Nigeria tun daga lokacin da ya karbi shugabancin kasarsa. Shugaba Ramaphosa na ganin Nigeria a matsayin kasa da take da mahimmanci ga kasarsa idan aka yi la’akari da rawar da ta taka wajen tabbatar da cewa Afirka ta Kudu ta samu ‘yanci kai.
Shugabannin biyu sun tattaunawa akan alamuran da suka shafi tsaro, zamantakewa, kasuwanci da kuma saka jari tsakanin kasashen biyu. Sun yi nazari akan fitowa da wani tsari na musamman da zai kawo daidaito tsakanin kasa da kasa.
A lokacin da suke ganawa da manema labaru Shugaban Afirka ta Kudu ya yi bayani game da karkashe ‘yan Nigeria da aka ce ‘yan kasarsa na yi. Yace lallura ce ta ta’addanci amma ba wai ana kashe ‘yan Nigeria ne domin suna kyamarsu ba. Saboda haka gwamnatin Afirka ta Kudu take gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk wadanda aka samesu da laifi domin gujewa kawo mummunar fahimtar al’ummarsu. Y ace dokar kasarsa bata wasa ko kadan wurin tabbatar da ta hukunta duk wani mai aikata laifuka.
Yayinda yake amsa tashi tambayar akan ko lokaci ya yi da zai rabtaba hannu akan kudurin cinikayya na kasashen Afirka wadda Nigeria ta ki sa hannu can baya, Shugaba Muhammad Buhari yace kasar nada lallurori irin na rashin aiki tsakanin matasa da kuma talauci ga al’umma da ya kamata ya yi la’akari dasu. Shugaban y ace idan ya bude harkokin kasuwancin kasar ga wasu kasashe matasa na iya fadawa cikin halin kunci saboda haka yake hattara kafin ya sa hannu.
A wani lokaci cikin wannan shekarar Shugaba Muhammad Buhari zai ziyarci Afirka ta Kudu.
A saurari rahoton Umar Faruk Musa
Your browser doesn’t support HTML5