Yau shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya ja kunnuwan masu hakan ma'adanan kasar ba bisa ka'ida ba su daina.
Daga yanzu gwamnatinsa ba zata amince da yadda masu hakan ma'adanai ke cin karensu ba babbaka ba. Kowa abun da ya ga dama yake yi lamarin da yace ya hana habakar sashen ma'adanai da hana samun kudin shiga yadda yakamata..
Shugaba Buhari ya ja kunnuwan mutane da babban lafazi bayan ya karbi rahoto daga ma'akatar ma'adanai da karafa a karkashin jagorancin babban sakataren ma'aikatar Baba Umar Faruk.
Shugaban ya amince cewa ma'adanai da karafa suna da mahimmanci a bunkasa tattalin arzikin kasar. Bangare ne da ka iya budewa kasar wata hanyar samun kudin shiga masu dimbin yawa. Shugaban ya nuna bacin ransa akan rahoton da Baba Umar Faruk ya mika masa.
Shugaban yace "wannan ne rahoto masi muni da na samu. Lamarin babban barazana ne ga kasar bayan Boko Haram saboda hakan ma'adanai nada tasiri wurin samarda aikin yi.
Shugaba Buhari ya cigaba da cewa "ba zamu bar wannan bangare mai mahimmanci ga samun ayyuka ba da kuma habaka tattalin arzikinmu"
Shugaba Buhari yace dole ne mu tashi tsaye akan yadda muke gudanar da kasar. Yace kuma zamu tabbatar hakan ya faru.
Tun farko babban sakataren ma'aikatar ya shaidawa shugaban cewa 'yan kasashen waje sun mamaye hakan ma'adanai ba bisa kan kaida ba.