Sabon umurnin Babban Bankin Najeriya na hana ajiya a asusun dala da ke kasashen ketare na gamuwa da suka daga jam’iyyar adawa ta PDP, wadda ta ce ai hakan tsari ne na gurguzu, wanda ke tauye ‘yancin ‘yan Najeriya, wadanda su ka fi sabawa da tattalin arziki mai sakin mara.
Kakakin PDP Olise Meto ya zargi jam’iyyar APC da tilasta ma ‘yan Najeriya amfani da tsarin tattalin arzikin da ya ce na kwaminisanci ne. Y ace duk wannan na faruwa ne saboda kasa samar da alkiblar tattalin arziki har bayan wata uku da kafa gwamnati. Y ace dama da gangan Shugaba Buhari ya ki saka ‘yan kasuwa a tawagarsa lokacin da ya kai ziyara Amurka kwanan nan, wanda ya kashe gwiwar masu sha’awar saka jari a Najeriya.
Ya ce, i, ya lura cewa takaita ma’amala da dala ko kuma adanar dala a bankunan Najeriya ya sad alar ta fadi a kasuwar Najeriya da fiye da dala 30 ta yadda dala daya a yanzu 210 ne a kasuwar canji bayan kuwa a ‘yan baya bayan nan sai da ta kai Naira 2045.
To saidai masu kare manufofin APC na ganin ‘yan PDP sun tsorata ne da irin ingantattun tsare-tsaren da gwamnatin Buhari ke bullowa da su. Alhaji Aminu Madaucin Bakori y ace ai kuwa Buhari Ikon-Allah. Y ace ko dai ka so Buhari ko kuma ka tsorata saboda rashin gaskiyarka. Shi ma Sabo Imam Gashuwa y ace gwamnatin PDP ta samu makudan kudade daga farashin man fetur amma ta barar da komai. Don haka, a cewarsa, PDP ba ta da dalilin sukar matakin tattalin arzikin da APC ke daukawa ba.