Shugaban Najeriya Ya Gana da Ministocinsa

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Jiya majalisar ministocin Najeriya tayi taronta na mako mako karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammad Buhari yayinda suka tattauna suka kuma yi nazari akan abubuwa masu mahimmanci guda biyu

Magana ta farko da shugaban yayi da ministocin ita ce ta harkokin sufuri tsakanin kasa da kasa. Magana ta biyu ta tallaka ne akan matakan da gwamnati zata dauka domin yaki da masu fasakwaurin kayan abinci dake yiwa sha’anin noma zagon kasa.

Ministan sufuri da jiragen sama na Najeriya Hadi Sirika yayi karin haske akan wadannan abubuwa biyu. Ya ce Najeriya ta kula yarjejeniya da kasar Canada akan zirga zirgan jiragen sama tsakanin kasashen biyu.

Dangane da sha’anin noma Hadi Sirika ya ce shugaban kasa yayi gargadi tare da tsawatawa ‘yan sumoga da su bari domin suna yiwa kasar zagon kasa. Idan kuma suka yi kunnen shegu gwamnati zata yi masu diran mikiya, inji Hadi Sirika.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Najeriya Ya Gana da Ministocinsac- 3' 39"