Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Yana So A Sake Tsarin Yaki Da Cutar HIV

Shugaban kasa Goodluck Jonathan

Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana damuwa game da ci gaba da yaduwar kwayar cutar HIV a kasarn, ya kuma ce zai fuskanci wannan kalubalar sosai.
Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana damuwa game da ci gaba da yaduwar kwayar cutar HIV a kasarn, ya kuma ce zai fuskanci wannan kalubalar sosai.

A cikin jawabinshi kan shirinsa na yaki da cutar sida a Nigeriya daga shekara ta 2013-2015, shugaba Jonathan yace tilas ne dukan cibiyoyi da kungiyoyi da kuma ma’aikatu dake aiki da nufin shawo kan cutar, su yi cikakken shiri su kuma samar da tsari mai ma’ana da zai taimaka a sami cimma nasara .

Ya kuma bayyana cewa, ana bukatar Naira miliyan dubu dari uku da talatin domin yakin cutar HIV tsakanin 2010 da 2015 a Nigeriya, kasar dake da mutane miliyan 3.4 dauke da cutar.

Shugaban kasar yace kawo yanzu an sami kimanin naira biliyan N198.5 wanda ya kasa ainun kan abinda ake bukata domin aiwatar da wannan tsarin na kawar da cutar HIV.

Bisa ga shugaban kasa, babu dan Nageriyan da za’a bari ya mutu da cutar HIV daga yanzu, kuma yace karuwar kwayar cutar maimakon raguwar ta ya nuna cewa akwai sauran aiki a gaba.