Shugaban Miyetti Allah Ya Je Zagaye Yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya

  • Hasan Tambuwal

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na kas, Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru

A kokarin da take yi na samar da dawamammen zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya da kuma bata-gari a cikin mambobinta, Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta fara zagayen jihohin Kudu maso Yammacin Najeriya a karkashin shugabanta na kasa, Alhaji Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru.

"Mafitar nan ita ce muke nema. Domin ba ka samun mafitar matsala ba tare da ka je ka zauna ka gane, tun da ciwo ne dabam-dabam,” inji Kiruwa.

A cewarsa, kowane bangare na da yanayin matsalarsa wanda hakan ne yasa ya dauki bangaren Yarbawa da Nupawa da na mutanen Borgu. Ya bayyana cewa irin yanayin da sarakunan Borgu ke zaune da Fulani da manoma cikin zaman lafiya ya yi matukar burgeshi.

Sannan ya ce, ya zo jihar Oyo inda ya lura cewa, Yarbawa mutane ne wadanda ba su son tashin hankali.

Shugaban da ke zagayen tare da wasu shugabannin kungiyar na jihohi da na kasa, sun lashi takobin yaki da ‘yan ta’adda kamar masu satar shanu, da mutane, da kuma fashi.

“Mai laifi bai da kabila, bai da addini. Mai laifi duka mai laifi ne. Ko kabilar Fulani ne ya yi laifi aka kamashi, a hukunta shi.


Kiruwa ya kuma ja hankalin makiyaya domin su hada kai.

“Lokaci yayi da mu zo mu hada kanmu, mu bar cutar kanmu muna rufe abun da ba gaskiya ba. Dole lokaci yayi da zamu zo mu bada goyon bayanmu ga yadda za mu yi don a gane bata-gari a cikinmu a kuma hukuntasu. Mai aikata laifi ko waye, ko dan waye, ko baban waye ne, a kamashi a hukunta shi.”

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Miyetti Allah Ya Je Zagaye Yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya - 3' 03"