Shugaban kwamitin majalisar dattawa da ke sa ido kan dakarun Amurka, mai karfin fada a ji, ya ce har yanzu akwai al’amuran da suka shige duhu dangane da harin kwantan baunar da ya kashe sojojin Amurka hudu a Jamhuriyar Nijar a ranar 4 ga watan Oktoba.
A jiya Alhamis ne, wasu manyan jami’an ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, suka gabatar da bahasi a gaban John McCain dan jam’iyar Republican da sauran mambobin kwamitin cikin sirri.
Wadanda suka gabatarda bahasin sun hada da Robert Karem, maitamakin sakatare kan harkokin tsaro na kasa da kasa, da kuma sojan sama Manjo Janar Albert Elton, wanda shi ne mataimakin darektan kula da fannin ayyukan kundunbala na musamman da kuma yaki da ta’addanci.
McCain ya bayyana cewa ya yi farin ciki da hadin kan da suka samu daga ma’aikatar tsaron ta Pentagon, amma kuma har yanzu akwai batutuwa da dama da yake son ya sani.
“Mene ne dabarar, kuma mene ne ya sa aka bamu mamaki? Akwai tambayoyin 100 da ke bukatar a amsa su,” McCain ya fadawa manema labarai.
Haka kuma Sen. McCain yace yana son a fahimtar da shi yadda aka kwashe har kwanaki biyu kafin a gano gawar Saje La David Johnson, daya daga cikin sojojin da aka kashen a Nijar.