Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa Juan Angel, Zai Fuskanci Zaman Gidan Kasu

Kotu ta daure tsohon shugaban hukumar kwallon kafa na kudancin Amurka Juan Angel Napout, a gidan yari na tsawon shekara tara, sakamakon samunsa cikin badakalar cin hanci da rashawa a hukumar kula da wasan kwallon kafa na duniya FIFa.

An same shi a watan Disamba na bara yana fuskantar shari'a a wata kotu dake karamar hukumar Brooklyn, a jihar New York. An zargi dan kasar Paraguaya din ne game da cin hanci da rashawa da wasu laifufuka biyu.

Kuma tsohon mataimakin shugaban FIFA ne, kuto taci taransa dalar Amurka miliyan $1m kimanin fan dubu (£ 767,000). Dan shekaru 60 da haihuwa an sameshi da laifi tare da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Brazil Jose Maria Marin.

Ku Duba Wannan Ma Yadda Ta Kaya A Gasar Neman Tikitin Shiga Wasannin Champions League

Marin, mai shekaru 86, shima an tsare shi a farkon wannan wata na tsawon shekaru hudu kuma zai biya tarar dala $1.2m kwatankwacin fan dubu (£ 920,000).

An kama Napout a gidan otel Baur Au Lac a Zurich a cikin watan Disamba na 2015, watanni bakwai bayan da aka fara kai bincike a wannan hotel din inda aka tsare jami'an FIFA guda bakwai, da ake tuhumarsa.

Laifukan da suka shafi Napout shine, sa hannu a cikin shirye-shirye kan karɓar miliyoyin daloli a cin hanci a musaya da kafofin watsa labarai,
da kuma cinikayya zuwa wasu wasanni na wasan kwallon kafa.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa Juan Angel, Zai Fuskanci Zaman Gidan Kasu 2' 20"