Dan kwallon Barcelona, Paco Alcacer ya koma Borussia Dortmund, a matsayin aro zuwa karshen kakar wasannin bana. Dan wasan mai shekarun 24 ya zo kungiyar Barcelona ne daga Valencia a shekarar 2016 kan kudi Euro miliyan 30 kimanin (£27.3m) amma ya kasa shiga cikin manyan ‘yan wasan kungiyar Barcelona.
Dortmund ta ce suna da ra'ayin sayen Alcacer kan kudi Euro miliyan 25 (£ 22.7m) a karshen kakar wasan bana, kungiyar Real Madrid ta ce tana sha'awar sayen dan wasan gaba na Manchester City, Raheem Sterling, mai shekaru 23, a duniya amma sai kakar wasa mai zuwa.
Har ila yau Real madrid tana bukatar sake dawo da Mariano Diaz daga Lyon ta hanyar kudin da suka kai yuro Miliyan 22 kimanin fan miliyan (£ 19.9m) sai dai Sevilla, zata amince da farashin Miliyon 35m (£31.8m kan sayar da dan wasan.
Barcelona, na son sayen dan wasan tsakiya kafin a rufe saye da sayarwar ‘yan wasa a ranar Laraba, amma kulob din ya yanke shawarar sayen dan wasan Manchester United Paul Pogba, mai shekaru 25 da haihuwa. Dan wasan gaba na Arsenal Alexandre Lacazette na Faransa, mai shekaru 27, da haihuwa yana duba makomarsa a Emirates.
Dan wasan Tottenham mai shekaru 28 da haihuwa Danny Rose, zai ki amincewa da yarjejeniyar komawa kungiyar Paris St-Germain a matsayin aro. Tsohon dan wasan Brazil da Real Madrid Ronaldo na shirin sayen kungiyar kwallon kafa ta Valladolid dake kasar Spain.
Real Betis, tana shirin daukar dan wasan dan kasar Brazil Rafinha mai shekaru 25, da haihuwa a matsayin aro daga kungiyar Barcelona. Dan kwallon Liverpool Sheyi Ojo, mai shekaru 21, a duniya na shirin komawa kungiyar Stade de Reims na Faransa a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasan bana bayan da dan wasan ya ce yana sha'awar komawa Ligue 1na kasar faransa.
Tsohon dan wasan Manchester City Yaya Toure, mai shekaru 35, a duniya yana kusa da shiga wani sabon kulob bayan da tsohon dan dan wasan Ivory Coast, ya yi gwajin lafiyarsa a London.
Fenerbahce ta musanta rahotanni da suke cewa tana kokarin shiga cikin sayen dan kwallon Tottenham Moussa Sissoko, mai shekaru 29.
Dan wasan Barcelona Gerard Pique, mai shekaru 31, da haihuwa ya ce ba shi da sha'awar komawa kungiyar Manchester United, da ke taka leda, dan wasan dai ya bar Old Trafford zuwa Nou Camp, a shekarar 2008.
Facebook Forum