Shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh ya nemi a gudanar da zabe kafin ya mika mulki

Shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh.

Shugaban Yemen Ali Abdullah Saleh ya bayyana himmar mika mulki cikin lumana ta wajen kaddamar da zaben shugaban kasa

Shugaban Yemen Ali Abdullah Saleh ya bayyana himmar mika mulki cikin lumana ta wajen kaddamar da zaben shugaban kasa.

A jawabinsa na farko ta talabijin ga al’umar kasar tun bayan dawowar ba zata da yayi cikin kasar , shugaba Saleh ya fada jiya lahadi cewa zai aiwatar da tsarin mika iko da majalisar kasashe dake yankin Gulf ta shimfida. Shirin wadda ya ci tura ya bukaci shugaba Saleh ya mika iko ga mataimakinsa.

Ranar jumma’a ce Mr. Saleh ya koma Sana’a babban birnin kasar, bayan zaman jinya na wata uku a makwabciyar kasar Saudiyya, daga raunuka da ya samu sakamakon wani yunkurin halakashi da aka so yi cikin watan Yuni.

Shugaba Abdullah Saleh yayi jawabin nasa ne sa’o’i bayan da dakarun kasar suka bude wuta kan wani gungun masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnati a Sana’a, suka jikkata mutane 17, an sami rahoton akalla mutum daya ya rasa ransa.

Shaidu suka ce masu zanga zanga suna maci ne kusa da shelkwatar sojojin kasar, a lokacin ne sojojin suka budewa masu zanga zangar wuta.