A wani shirin gidan talabijin da aka watsa a kasar, babban sakataren hukumar zaben Rwanda, ya ce sama da kaso 80 cikin 100 na masu rijistar kada zabe a kasar, sun jefa kuri’unsu a yau Juma’a.
Cikin watan Yuli, Kagame ya fada a wajen wani gangamin kamfen cewa zaben shugaban kasar zai zamanto cikin tsari. Wannan babban rinjaye da shugaban ke da shi a zaben karon farko na nuni da cewa zai sami damar ci gaba da shugabancin kasar a karo na uku.
A babbar hedikwatar jam’iyyar Kagame ta R-F-P, dubban shugabannin siyasa masu goyon bayan shugaban ke kallon sakamakon zaben dake shigowa daga sassa daban daban na kasar ta wani katon majigi.
Kagame dai ya share shekaru 17 a kan karagar mulki izuwa yanzu. Wani zaben raba gardama da aka gudanar a shekarar 2015, ya baiwa Kagame damar tsayawa takarar shugabancin kasar har sai shekarar 2034.