Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da kanfen neman zabe

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan (C),tare da matarshi Patience (R), Mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, yana dagawa jama'a hannu kafin kaddamar da kamfen dinsa a Abuja.

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da kamfen tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar cikin watan janairu.

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da kamfen tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar cikin watan janairu. Mr. Jonathan ya sanar da haka ne jiya Asabar a gaban dubban magoya bayanshi da suka hallara a birnin tarayya Abuja. Ranar Laraba shugaban kasar yayi amfani da shafin musayar ra’ayoyinsa na Facebook wajen sanar da niyarsa ta tsayawa takara. Watanni hudu da rantsar da shi a matsayin shugaban kasa bayan rasuwar zababben shugaban kasar Najeriya, Mr. Jonathan ya shaidawa magoya bayansa cewa kasar tana cikin wani yanayi na canji. Bisa ga cewarshi, zai tsaya takara ne sabili da ya hakikanta cewa, zai iya jagorantar kasar zuwa samun wannan canjin.

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da kanfen neman zabe

Shugaban kasar ya dubi dubban magoya bayansa da suka hallarci bukin kaddamarwar yace, “wannan ba taron jama’a bane kawai, tamkar juyin juya hali ne.” kashi biyu bisa ukun gwamnonin kasar sun halarci bukin kaddamarwar. Ana tababa kan takarar shugaban kasar kasancewa ya sabawa tsarin karba karba na jam’iya mai mulki dake cewa, ya kamata shugaban kasa na gaba ya fito daga arewacin kasar.