Shugaban kasar Misira ya kare baiwa Saudiya wasu tsibirai biyu

Shugaban Misira Abdel-Fattah el-Sissi

Shugaban Misira Abdel-Fattah el-Sissi ya fito ya kare bada wasu Tsibirai guda 2 ga Saudiyya a jiya Laraba, sannan ya karyata cewa jami’ansu na sirri ne ke da alhakin kashe dalibin nan dan kasar Italiya.

Shugaban ya fito gidan talbijin don tabbatarwa Misirawa cewa ba bada ko wane bangare na kasarsu ga wata kasa ba, ya kara da jaddada cewa, “Bari mu yi maganar nan gaba daya ma ku ji, ‘yan Majalisar da kuka zaba ne za su tattauna amincewa da wannan ko kuma a’a.

Gwamantin Alkahira dai ta sanar da maidawa Saudiyya wasu tsibiran dake gabar tekun Maliya Sanafir da Tiran, wanda El-Sissi yace dama can na Saudiyyar ne da ta bawa Masar ikon kulawa da su a shekarar 1950, sakamakon fargabar mamayar Isra’ila a lokacin.

Wasu ‘yan kasar sun zargi shugaban da cewa ya sayar da wanin yankin Masar ga Saudiyya ne kawai don neman taimakonta. Wani dan Majalisa da ya nemi tambayar el-Sissi game da lamarin a lokacin taron manema labarai, sai ya dakatar da shi da cewa, “Ban bawa kowa izinin wannan maganar ba”. Yana fada aka katsa shirin talbijin din da ake kallo.