Shugaba Patrice Talon wanda ya yada zango a birnin Yamai bayan kammala wani taro da suka gudanar a birnin Dakar na kasar Senegal wanda ya hada ministocin kudi da na tsaro, da kwamandojin rundunonin mayakan kasashen Afrika ta yamma renon Faransa, ya zo ne domin sanar da shugaban kungiyar CEDEAO Issouhou Mahamadou na Nijer cewa kasashe mambobin UEMOA sun yanke shawarar bayar da gudunmowar kudi dala miliyan 500 akan billion 1 da kungiyar ECOWAS ta kudiri aniyar kashewa domin yaki da ta’addanci.
A ra’ayin Ibrahim Kantama, wani mai sharhi akan al’amuran yau da kullum, matakin kasashen na UEMOA, ya yi dai dai saboda a cewarsa, alama ce dake nunin shuwagabanin kasashen Afrika sun fara gane muhimmancin hadin kai.
Haka kuma, koma bayan da matakin rufe iyakokin Najeriya ke ci gaba da haddasawa al’umomin tarayyar Najeriya da makwaftanta na daga cikin batutuwan da shuwagabnin biyu suka tattauna akai.
Patrice Talon ya ce wannan magana ce dake damunmu mu duka to amma muna kyautata zaton nan ba da jimawa ba kwararrun kasashen mu zasu bullo da hanyoyin da zasu bada damar daidaita al’amura.
A nan masu sharhi na ganin akwai bukatar sake duba wannan mataki na gwamnatin Najeriya.
Ayyukan shimfida bututun mai a tsakanin kasashen Nijer da Benin, da batun farfado da ayyukan shimfida hanyar jirgin kasa na daga cikin batutuwan da shugaba Issouhou mahamadou da takwaran aikin sa Patrice Talon suka zanta akansu a yayin wannan ganawa.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5