Da alama shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya kama hanyar sake lashe kuri'un da ake gaddama akai bayan da babban abokin hamayyarsa yace zai janye daga takarar.
Tunda aka riga aka kidaya kusan kashi tamanin na kuri'un da aka kada a zaben ranar Lahadi da ta gabata a wannan kasa dake Yammacin Afirka shugaba Conde zai lashe zaben da gagrumar nasara.
Ana kyautata zaton za'a bada sakamakon zaben gaba daya yau Juma'a.
Babban abokin hamayyar shugaban Cellou Dalein Diallo ya janye daga takarar ranar Laraba yana cewa ba zabe aka yi ba magudi aka tafka. Kawo yanzu ba'a sani ba ko janyewarsa zata tilasta a yi zaben zagaye na biyu.
Jiya Alhamis kungiyar Human Tights Watch ta gargadi jam'iyyun siyasa da su yi taka tsantsan su kaucewa tashin hankali. Kungiyar ta kuma kira jami'an tsaro su tabbatar babu tashin hankali ko karya doka da oda.
Dama ita kasar Guinea ta yi kamarin suna wajen tashin hankali da harzuka zaman dar dar bisa ga kabilanci lamarin da ya kan hallaka mutane da dama saboda rigingimun siyasa.