Shugaban Kasar Gabon Ya Nada Firai Minista Dan Arewa

Shugaban kasar Gabon Ali Ben Bongo Ondimba

Shugaba Ali Bongo ya nada tsohon ministan aikin gona Raymond Ndong Sima a mukamin firai minista

Shugaban kasar Gabon ya zabi sabon firai minista daga wani yankin da ba a taba baiwa wannan mukami ba.

Da yammacin jiya Litinin shugaba Ali Bongo ya yi sanarwar cewa ya nada tsohon ministan aikin gona Raymond Ndong Sima a mukamin firai minista.

Mai baiwa shugaban kasar ta Gabon shawara, Igor Simard ya shaidawa sashen Turancin Ingilishin Muryar Amurka cewa an zabi Raymond Ndong Sima a matsayin firai ministan ne saboda ya na da sani a fannin gwamnati, da kuma fannin kamfanoni masu zaman kan su, kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da shirye-shiryen tattalin arzikin shugaban kasar.

Simard ya ce ga al’ada duka firai ministocin da aka yi a kasar Gabon sun fito ne daga yanki daya, wato Libreville babban birnin kasar, ya ce a wannan karo shugaban kasar ya na so ya kawo wani muhimmin canji ne, shi ya say a zabi wani haifaffen yankin Woleu Ntem na arewacin kasar.

Simard ya ce wannan wani babban abun ba zata ne wanda kuma ke kunshe da wani kyakkyawan sako ga daukacin al’ummar kasar Gabon, na nuna mu su cewa kowa ma na iya rike mukamin firai minista a kasar.