Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai yana zargin Amurka da kin bada hadin kai a binciken da ake gudanarwa kan kisan gillan da ake zargin wani sojan Amurka da yiwa wadansu kauyawa 16.
Shugaba Hamid Karzai ya gana da shugabannin kabilu da iyalan mutanen da aka kashe a bude wutar da sojan yayi a lardin Kandahar ranar Lahadi. Ya bayyana yau Jumma’a cewa, tawagar da ya tura domin bincike kisan, bata sami hadin kan da ya kamata daga jami’an Amurka ba.
Mr. Karzai ya bayyana cikin fushi cewa, ”an jima ana kashe farin kaya, kuma tura ta kai bango yanzu”. Ya kuma ce “ba zasu lamunci ci gaba da wannan halin ba”.
Shugaban kasar Afhanistan din ya kuma bayyana shakkun bayanin da rundunar sojin Amurka ta bayar cewa, soja daya ne ya kashe mutanen. Kauyawan sun ce sojoji fiye da daya ne suka kai harin a yankin Panjwai inda aka kashe mutane da suka hada da kananan yara