Shugaban Kamfanin Google Zai Gurfana A Gaban Majalisar Dokokin Amurka

Ranar juma’a ne wani babban dan jam’iyar Republican ya ce shugaban kamfanin Google, Sundar Pichai ya amince ya gurfana a gaban kwamitin shari’a na Majalisar Wakilan Amurka a cikin wannan shekara da muke ciki akan damuwar da ‘yan jam’iyar Republican, suka nuna cewar kamfanin yana nuna bambanci akan ra’ayin ‘yan mazan jiya.

‘Yan jam’iayar Republican, suna so su tambayi kamfanin Google, ko na’urar bincikenta ta haruffa na tasiri akan bil’adama. Suna kuma so su bincike shi a kan batutuwan sirri, rarraba labarai da ra’ayi, da kuma yin hulda da kasashen da ke cin zarafin ‘yan adam.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Amurka, Kevin McCarthy, ya ce Pichai, ya hadu da wasu manyan ‘yan jam’iayar Republican, ranar juma’a don tattaunawa akan wannan damuwa. Sannan ya fadawa ‘yan jarida bayan taron da cewa wannan ganawa tayi ma’ana kwarai da gaske domin an fadawa juna gaskiya.

McCarthy, ya ce “Ina tsammanin mu nuna cewa babu wani bambanci, wanda shine yanayin mutum, amma dole mu kasance masu gaskiya da adalci, kamar yadda hanyar fasahar kasuwanci ke bunkasa, ba nu da isasshiyar gaskiya kuma wannan ya haifar da rushewar amana kuma hakan iya zai cutar da masu amfani”.

Bangaren harrufa na Google ya karyata game da nuna bambanci akan ra’ayin ‘yan mazan jiya, Pichai yabar wajan taron ba tare da ya ce komai bai.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Kamfanin Google Zai Gurfana A Gaban Majalisar Dokokin Amurka 1' "48"