Shugaban Juyin Mulki a Burkina Faso Ya Nemi Ahuwa

Shugaban juyin mulki a kasar Burkina Faso Janar Gilbert Diendere.

Jiya Litinin, Shugaban sojojin da suka yi juyin mulki makon da ya wuce a Burkina Faso ya nemi afuwar ‘yan kasar da cewa, zai mika mulki ga gwamnatin farar hula.

Janar Gilbert Diendere ne ya fadi haka a wata sanarwa a jiyan. yace zai sauka a matsayinsa na shugaban kasar da zarar an cimma karshen tattaunawar shiga tsakani.

Wanda kungiyar kasashen Africa ta yamma wato ECOWAS ta kira cikin gaggawa don a zauna a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya game da lamarin.

Janar Diendere shugaban masu tsaron shugaban kasar da ya hambare,ya fadawa sashen faransancin Muryar Amurka cewa, ya yi haka ne don gujewa zubar da jini.

Yace tsohon shujgaban kasar Jean-Baptiste Oued’rao’go a yanzu haka yana cikin masu tattaunawar neman mafitar da za a yi.

Sannan sojojin sun ce sun bada damar sakin Firaministan rikon kwaryar kasar da aka yiwa daurin talala a gida tun bayan juyin mulkin.

A baya dai rundunar sojojin Burkina Faso tace tana tunkarar babban birnin kasa Ouagadougou don tabbatar da cin nasarar sa sojojin gadin da aka fi sani da RSP su ajiye makamansu.

Kakakin rundunar sojan kasar Kaftin Herve-Ye ya fadawa sashen Faransanci na Muryar Amurka cewa, bukatar su sojojin shi ne su mika wuya, su kuma tasa keyar wadanda suka yi juyin mulki zuwa barikin soja dake kusa da wani dandalin taruwar jama’a.

Wakiliyar Muryar Amurka Emilie Yob tace tuni sawu suka dauke daga titunan birnin jin cewa sojojin kasar na tafe.