Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kori ministan kudinsa a jiya Laraba, saboda takaddama kan kasafin kudi, lamarin da ya rusa gwamnatin hadin gwiwa ta jam’iyyu uku, wanda hakan ya sa ‘yan adawa su ka shiga kiran da a gudanar da zaben gaggawa.
Scholz ya kori ministan kudi kuma shugaban jam’iyyar FDP, Christian Linder biyo bayan wata doguwar tattauwanawa mai cike da takaddama wadda aka yi da nufin daidaita gibi a kasafin kudin kasar.
Linder da jam’iyyarsa sun yi watsi da karin haraji da kuma neman a rage shirye-shiryen zamantakewa, ra’ayin da sauran mambobin kawancen biyu suka yi watsi da shi.
Jam’iyyar FDP wani bangare ne na kawancen gwamnatin tare da jam’iyyar SPD ta Scholz da jam’iyyar Green Party, wadanda aka hade bayan zabubbukan 2021.