Shugaban hukumar leken asiri ta Amurka, wato CIA, Mike Pompeo ya kai wata ziyara birnin Pyongyang cikin sirri, inda ya je domin ganawa da shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un, a cewar wasu majiyoyin kafafen yada labarai.
Wannan ziyarar sharar fage ce ga tattaunawa ta kai-tsaye da za a yi tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa, Kim, wacce ta gudana a lokacin bikin Easter, a cewar wasu jami’ai da ba a bayyana sunansu ba a kafofin yada labaran da suka ruwaito labarin.
Tun da farko da ma, shugaba Trump ya taba bayyana cewa Amurkan ta tattaunawa da shugabannin Korea ta Arewan.
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne, yayin da yake karbar bakuncin Firayi Ministan Japan, Shinzo Abe a jihar Florida.
Sai dai ba tare da bata lokaci ba, Sakatariyar yada labarai a Fadar gwamnati ta White House, Sarah Huckabee Sanders, ta musanta cewa wata ganawa ta kai-tsaye ta wakana tsakanin Trump da Kim ko kuma da wasu manyan jami’an Korea ta Arewa.
Tun gabanin haka dai, Firayi Minista Shinzo Abe, ya yabi Trump, saboda amincewa da ya yi ya tattauna da Kim.
ACT 2: Firayi minister Abe kenan yake cewa “Zan iya tabbatar muku da cewa, matsayar da Amurka ta dauka, kan yadda za mu ci gaba da tursasa Korea ta Arewa, mun himmatu domin ganin mun warware shirin mallakar makamin nukiliyan kasar da aka tabbatar tana yi.”
A baya, shugaba Trump ya taba cewa yana sa ran zaman tattaunawar da Korea ta Arewa, zai wakana ne a farkon watan Yuni ko kuma gabanin hakan.