Shugaban Hukumar Kwallon kafar kasar Sifaniya da aka dakatar daga aiki Luis Rubiales, ya ajiye aikinsa.
An dakatar da Rubiales ne bayan da ya sumbaci daya daga cikin ‘yan wasan kasar Sifaniya ta mata da suka lashe kofin gasar cin kofin duniya da aka kammala.
Yayin da ake bikin ba da kyaututtuka ne Rubiales ya sumbaci Jenni Hermoso a labbanta ba tare da izininta ba.
Hakan ya sa aka dakatar da shi a lokacin aka kuma yi ta kiraye-kirayen da ya ajiye aikinsa amma ya ki.
Sai dai a ranar Lahadi, Rubiales ya bayyana yin murabus a wani sako da ya wallafa a shafin X (Twitter.)
Sifaniya ta doke Ingila a wasan karshe da ci 1-0 a ranar 20 ga watan Agusta a gasar wacce New Zealand da Australia suka karbi bakunci.
A halin da ake ciki, masu shigar da kara sun gabatar da bukatar tuhumar Rubiales da aikata laifi a gaban kotun kasar ta Sifaniya.
Hakan ya faru ne kwanaki kadan bayan da Hermoso ta zargi shi da cin zarafinta ta hanyar neman yin lalata.
Dan shekaru 46, tun daga shekarar 2018 Rubiales yake jagorantar hukumar kwallon kafar ta Sifaniya.
Tuni dai kungiyar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da shi daga aikinsa a hukumar.
Rubiales ya kuma sanar da ajiye aikinsa na hukumar zakarun kwallon kafar nahiyar turai ta UEFA inda yake rike mukamin mataimakin shugaban hukumar.