Farfesa Yakubu, wanda ya sake nanata yawan rijistar da a ka raba da masu kada kuri’a miliyan 72 da yawan runfunan zabe, ya ce kowa na da izinin zuwa rumfar zabe da wayar salula ya dau hotuna amma ban da cikin zagaye na dangwala kuri’a.
Shi ma babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya halarci taron hukumar zaben da ba da tabbacin kula da tsaro a dukkan lokacin zaben.
Adamu ya ce jami’an tsaro za su halarci tashoshin zabe amma ba tare da makamai ba don haka ba bukatar wata firgita ga jama’a.
Duk da hakan na nuna ba zullumin bindige duk wanda ya yi yunkurin satar akwatin zabe kamar yadda shugaba Buhari ya sanar, babban sufeton ya ce za a damke duk wanda ya nemi haddasa fitina da gurfanar da shi gaban kotu.
Dan majalisa dattawa Sanata Yahaya Abdullahi daga Kebbi ya bukaci ‘yan bangar siyasa su gujewa tada husuma.
Taron na karshe gabanin zabe ya samu halartar masu duba zabe na kungiyar Afirka ta yamma ECOWAS karkashin jagorancin tsohuwar shugabar Laberiya Ellen Johnson Sirlief.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5