Wannan na zuwa ne lokacin da ake ganin ‘yan kabilar ta Fulani a sahun gaba wajen aikata ayyukkan ta'addanci da ‘yan bindiga ke yi, duk da yake sun ce ba Fulani ne kadai ke aikata ta’addanci ba.
An jima ana yi wa kabilar Fulani wani kallo na daban a wasu sassan Najeriya, abin da kuma ba ya rasa nasaba ga yadda ake samun su da yawa cikin ayyukkan ‘yan bindiga har ta kai ga suma na fuskantar tsamgwama a wasu wurare.
Sai dai jagororin kabilar ta Fulani sun ce suna da kyawawan dabi'u da aka san su da su wadanda da ‘yan kabilar sun rungume su hannu biyu, da yanzu wani zance ake yi ba kallon Fulani da ta’addanci ba.
Dokta Usman Abubakar Kokoshe na daya daga cikin jagororin Fulani, kuma shi ne shugaban Sashen Nazarin Fulatanci a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, ya ce idan aka duba kowace kabila ana samun baragurbi cikinta, kuma ya san cewa ana samu wasu daban.
Wannan yunkurin da shugabannin kabilar Fulani ke yi yanzu da suka kira ‘PULAAKU’ abu ne da ake sa ran ya sauya tunanin Fulani su san tafarkin da ya dace a ce suna a kai, sabanin yadda wasunsu ke gudanar da rayuwarsu a yanzu.
Abdullahi Musa daya daga cikin jagororin Fulani yana ci gaba da kiran ‘yan kabilar Fulani wadanda ba bisa hanya ba su dawo kan kyakkyawan tafarki.
Masana dai daga cikin Fulanin na ganin akwai hanyoyin da idan aka bi su za’a samu fahimtar Fulani da halayensu ta yadda za' a daina ganin masu aikata laifi da cewa Fulani ne.
Sufyanu Muhammad Goshe na Jami'ar Koyar da Aikin Malanta ta Shehu Shagari da ke Sokoto ya ce hakan ya dace domin a daina alakanta kowane aiki ga kabilar.
Samun nasarar rungumar kyawawan dabi'u na Fulanin wata kila kan iya sa a daina kallon su da masu aikata laifukan ta'addanci ko akasin haka.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5