Shugaban A murka Donald Trump yace Gwiwar sa tayi sanyi a lokaci da yake jawabi wajen bikin bude cibiyar adana kayan tarihi na masu fafitikar kare hakkin bil adama da akayi a Jackson, dake Mississippi, inda yayi jawabi yabawa tsoffin shugabanin kare hakkin bil adama irin su Medger Ever da Reverend Martin Luther King Junior.
Sai dai kasancewa shugaban a wannan wurin biki ya haifar da rudani cikin masu suka lamirin sa.
Abinda suke cewa ko shine shida ya ruruta wutar nuna banbancin launin fata anan Amurka kuma yanzu shine ke yaba wadanda suka yi fice a sukan wannan bakar al’ada wannan lamari akwai daure kai.
Daya daga cikin masu wannan raayin ko sun hada da dan majilisar dokoki Amurka, John Lewis wanda da farko aka shirya zaiyi jawabi a wajen wannan taron amma kwaran sai ranar alhamis yace ba zai halarci taron ba bayan da ya samu labarin shugaba Donald Trump yace zai halarci taron.
Sai dai Trump bai kambama taron ba yayi jawabin sa.
Wadanda sukahalarci taron sun hada da matar marigayi Ever da kuma Ben Carson wanda yake shine sakataren harkokin gidaje da muhalli a gwamnatin ta Trump, daga karshe yace muna matukar godiya ga wanda ya samar da wannan cibiyar kuma kana burge mu.
Shiko a nasa jawabin gwamnan jihar ta Mississippi Phil Bryant wanda dama mai goyon bayan shugaba Trump ne kuma shine ya gayyace shi wajen taron yace, wannan wata babban rana ce ga dukkan mu dake nan, Yace halartan wannan bikin bude wannan wurin adana kayan tarihin yan yakin neman yanci zai janyo hankalin duniya, kuma ya kara wa wannan cibiya kwarjini.