A ranar Litinin shugaba Mohamed Bazoum ya fara ziyarar aiki a Jamhuriyar Benin, inda aka shirya zai tattauna da takwaransa Patrice Talon, don neman hanyar magance matsalar tsaro dake addabar kasashensu.
Kashi 49 daga cikin 100 na kayayakin da ake safararsu zuwa jamhuriyar Nijar suna sauka a tashar jiragen ruwa ta Cotonou, hakan ya sa shugaba Bazoum ware lokaci na musamman don ziyarar gani da ido tare da ganawa da dubban ‘yan kasarsa dake gudanar da harkokin kasuwanci.
Gwamnatin Biden ta Amurka ta kuduri aniyar kashe dalar Amurka miliyan 500 don gudanar da ayyukan raya karkara a wani shiri na hadin gwiwar kasashen Nijer da Benin da aka yiwa lakabi da Program Compact.
Shirin na daya daga cikin batutuwan da aka shirya shugabannin biyu zasu tattauna kafin su dunguma zuwa tashar Seme da Nijer za ta yi amfnai da ita wajen sarafar Man Fetur zuwa kasuwannin duniya. Yanzu haka an kammala aikin shimfida bututun Mai daga Nijer zuwa Benin.
Kasashen makwabta ta bangaren kafafaren gandun dajin Parc National du W na fama da hare-haren ta’addanci sanadiyar tabarbarewar al’amura a Burkina Faso da Mali, babban dalilin da ya sa tawagar kasashen biyu za su tantauna don ganin bakin zare matsalar.
Sabon shirin kamfanoni da masana’antun da ake kira Glo Djigbe Ze, wadda shugaba Patrice Talon ya gina a da’irar Abomey Calavi da zummar bunkasa albarkatun noman al’ummar kasar Benin na daga cikin wuraren da shugaba Bazoum zai leka ya kafin ya karkare da wata ganawar da zai yi da daukacin ‘yan Nijer mazauna Benin.
Domin Karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Your browser doesn’t support HTML5