Garin Ramadi a Iraki na daya daga wuraren da ke fama da rikicin ta'addanci a kasar wanda ake ta fafatawa da mayakan Shi'a.
WASHINGTON D.C —
Shugaban Amurka Barack Obama, ya jaddada aniyarsa ta taimakwa Firai ministan Iraqi da kuma tsara wani shiri dai zai taimaka wajen kwato garin Ramadi, yayin da darakun Iraqin da mayakan ‘yan Shi’a suka taru a Yammacin birnin.
A baya dai, dakarun da mayakan na Shi’a, sun samu nasarar kwato garin Tikrit, sai dai Kakakin hukumar tsaron Amurka ta Pentagon, Kanar Steve Warren, ya ce akwai babban kalubale a gaba, idan aka yi la’akkari da cewa dakarun na Iraqi sun bar manyan makaman Amurka a baya a lokacin da suke tserewa daga birnin.
Wani mai sharhi kan al’amuran yankin, Ben Connable, ya ce barin tankunan yakin da aka yi a baya, zai iya kawo cikas ga yunkurin kwato garin na Ramadi.