Shugaban Amurka Yayi Nadamar Ceto 'Yan Wasan Kwallon Kwando Uku daga China

'Yan wasan kwallon kwando daga Jami'ar UCLA da aka samesu da laifin sata a wani shago a kasar China

'Yan wasan kwallon kwando uku an samesu da sata ne a wani kanti a China kafin shugaba Trump ya cetosu amma mahaifin daya daga cikinsu ya ce shugaban Amurka bai taka wata rawar a zo z gani ba wajen cetosu

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce da ma ya bar ‘yan wasan kwallon kwandon nan uku, da aka samu da laifin sata a wani kanti a kasar China, su cigaba da zama a gidan yarin Chinar, bayan da mahaifin daya daga cikin yaran ya ce Trump bai taka wata rawar kirki ba a sako da yaranaka yi.

Yaran uku, masu wasa ma Jami’ar California da ke Los Angeles, sun jinjina ma Trump a makon jiya saboda rawar da ya taka a sakin nasu, inda kai tsaye Trump ya roki Shugaba Xi Jinping na China alfarma ya sa baki, lokacin da shugabannin biyu su ka gana a wannan watan a Beijing.

To amma mahaifin LiAngelo, LaVar Ball ya yi watsi da rawar da Trump ya taka a sakin yara ukun da aka yi, wadanda aka tsare su a wani otal bayan ko takwarorinsu sun dawo Amurka.

A martanin da ya mayar ta kafar ‘twitter’ jiya Lahadi, Trump y ace, “Yanzu da ‘yan wasan kwallon kwandon uku suka samu ficewa daga China aka kuma kubutar da su daga daurin shekaru barkatai, LaVar Ball, mahaifin Li Angelo, na yin watsi da abin da na yi ma dansa ya na cewa sata a kanti ba wani abu ba ne. Da na bar su a tsare!”

An dakatar da dukkannin ‘yan wasan daga kulob din UCLA har sai illa ma sha Allahu.