Shugaban Amurka Donald Trump ya fada jiya Lahadi cewa ya kamata a maida mutanen dake shigowa Amurka ba bisa ka’ida ba kasashen su, ba tare da sa hannun alkalai ko zaman kotu ba.
WASHINGTON D.C —
A wasu rubuce-rubuce da ya kafe a shafinsa na Twitter, Trump ya ce, bai kamata mu bar wadannan mutanen su mamaye kasar mu ba….’ yana mai nuni da cewa tsarin Amurka ba ya bin kyawawan manufofin shige da fici da kuma doka da oda.
Shugaban na Amurka yayi ikirarin cewa yanzu duniya na yiwa tsarin shige da ficen Amurka dariya, ya ce ba a yiwa wadanda suka shigo kasar bisa kai’ida, suna kuma cigaba da jiran takardunsu shekara-da-shekaru adalci ba.
Kungiyar kare hakkokin jamm’a ta Amurka da ake kira American Civil Liberties Union da turanci, ta maida martani akan sakonnin na Trump, tana mai cewa tsarin da Trump ke so ya bi ya sabawa tanadin da kundin tsarin mulkin Amurka yayi akan kare jama’a.