Shugaban Amurka Donald Trump ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Koriya ta Arewa zai yi matukar bunkasa, sannan ya yi alkawarin kare iyalin Kim da ke mulkin kasar da abin da ya kira “cikakkiyar kariya” ta yadda gidan zai cigaba da mulki - muddun Kim ya amince ya rabu da makamin nukiliya. Trump ya yi gargadin cewa Idan ko Shugaba Kim Jong Un ya ki amincewa da wannan yarjajjeniyar, to za a yi kaca-kaca da wannan matalauciyar kasa.
A wani sabon bayani a jiya Alhamis, Shugaba Trump ya yi hasashen cewa canza lafazi da Koriya Ta Arewa ta yi wannan satin game da taron da aka shirya yi tsakanin shi Trump din da Kim ranar 12 ga watan Yuni a Singapore, na iya zama sakamakon ganawar da aka yi tsakanin Kim da Shugaban China Xi Jinping.
“Mai yiwuwa Shugaba Xi ke zuga Kim Jong Un,” a cewar Trump yayin da ya ke tattaunawa da Jens Stoltenberg, Sakataren Kungiyar Tsaro ta NATO kuma a gaban ‘yan jarida.
Trump ya kara da cewa, muddun aka soke wannan ganawar, “za mu yi amfani da zabi na gaba.”
Trump ya ce har yanzu jami’an gwamnatocin Amurka da Koriya Ta Arewa na tattaunawa kan tsarin ganawar da ake shirin yi din tamkar babu wata matsala duk kuwa da wasu kalaman da ke fitowa daga Koriya Ta Arewar da ke jefa ayar tambaya kan yiwuwar ganawar.