A wani jawabi da aka dade ana jiran jinshi, Shugaban Amurka ya fito fili ya bayyana shirin yaki da miyagun kwayoyi da ka hada da hukumcin kisa
WASHINGTON DC —
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana wani shiri jiya Litinin, da aka dade ana jira, na shawo kan matsalar miyagun kwayoyi.
A wani jawabi da ya gabatar a Manchester jihar New Hamshire, Trump yayi alwashin samar da yanayi da yara zasu girma ba tare da fuskantar matsalar miyagun kwayoyi ba, yace, “zamu hada hannu mu shawo kan dogaro ga miyagun kwayoyi a Amurka baki daya”.
Trump yace idan ana so haka ta cimma ruwa, tilas ne a shiga kafar wando daya da dillalan miyagun kwayoyi.
Yace, “idan bamu tsaya da gaske kan masu safarar miyagun kwayoyi ba, aikin banza muke yi. Matakin da za a dauka kuma ya hada da aiwatar da hukumcin kisa”.